1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenyata na kan gaba a zaben kasar kenya

March 5, 2013

Al'umar Kenya na ci gaba da jiran sakamakon zaben gama gari da aka gudanar a kasar. Sakamakon farko na zaben shugaban kasa na nuni da cewa wanda gwamnati ta tsayar Uhuru Kenyata ya tserewa Raila Odinga da yawan kuri'u.

https://p.dw.com/p/17qxE
Hoto: Getty Images

Ya zuwa yanzu dai an gama kidaya kashi 40% na runfunar zabe kimanin dubu 32 da aka mika sakamakon kuri'un da aka kada a cikin su. Bisa ga wannan kididdiga dai Uhuru Kenyata ya lashe kimanin kaso 53% na kuri'un zaben shugaban kasa, yayin da firaminista Raila Odinga ke bi masa baya da kaso 41% na yawan kuri'un da aka kada.

Tuni dai tawagogin da suka sanya Idanu kan zaben suke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da yiwuwar barkewar rikici bayan bayyana sakamakon karshe na zaben. Har ya zuwa yanzu dai babu tabbas ko ya Allah Al'mmar kenya sun dauki darasi daga rikicin zaben da ya gudana a shekara ta 2007 wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama. Wani mai fashin baki kan Al'amuran siyasa kasar ta Kenya Ahmad Rajab ya shaidawa Dw a Nairobi babban birnin kasar ta Kenya cewa ya yi da kamar wuya a mayar da bara bana.

Wahlen Kenia
Hukumar zabe ta kyautata tsari domin a gujewa tashin hankaliHoto: DW

" A jiya in ka tambayi masu kada kuri'a ra'ayoyinsu kowa na bayyana cewa zaman lafiya zaman lafiya, Ina ganin Al'ummar kasar sun dauki darasi daga rikicin da ya barke a zaben shekara ta 2007, wanda hakan ya sanya ba sa fatan hakan ta sake faruwa"

Shi kuwa tsohon shugaban kasar Mozambik wanda kuma shine ke jagorantar tawagar sanya idanu ta kungiyar Gamayyar Afrika, Joaquim Chissano cewa yayi, sun yi nazarin sakamakon da dukkanin kungiyoyi da suka lura da yadda zaben ya gudana suka bayar, tun daga kungiyar Commonwealth da IGAD da COMESA har ya zuwa ga cibiyar Carter da ofishin jakadancin Amirka da dai sauransu. kuma ya na nuni da cewar ya zuwa yanzu, babu wani dalili na nuna damuwa game da zaben.

Kenia Wahlen Raila Odinga
So uku Raila Odinga ya tsaya taka a zaben shugaban kasa a KenyaHoto: Reuters

"Ba mu da wani dalili na nuna damuwar ko za'a sami tashin hankali. Shugabannin siyasar kasar sun yi alkawarin cewar ba za su kyale ayi amfani da tashin hankali ba, inda za su gwammace su kai kararrakinsu gaban kotu, idan har ba su yarda da sakamakon zaben ba. Kafofin yada labarai su ma suna taimakawa, haka nan kungiyoyin kare hakkin jama'a da coci coci a kullum su na kira ga jama'a su zauna lafiya, su kuma kaucewa duk wani tashin hankali".

Kwamishinan Hukumar zaben kasar James Oswago ya ce ya zuwa yanzu babu wani dalili da zai sanya Jama'a su fara korafi kan zaben.

Kenia Wahl 2013
Uhuru Kenyatta na fatan zama shugaba na gaba a KenyaHoto: DW/J.Shimanyula

"Har ya zuwa yanzu bamu samu sakamakon farko na kuri'un da aka kada daga tashoshin zabe dubu 23 ba, ya zuwa yanzu mun samu sakamakon kaso 30 cikin dari ne kawai. Kamar yadda nace a jiya wannan sakamako ne na farko, ba shine sakamakon karshe da hukuma ta amince da shi ba, sa bo da haka kada wanda yayi murna haka nana kuma kada wanda yayi korafi"

Shi dai Uhuru Kenyata kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa na tuhumarsa da laifin iza wutar rikicin da ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu daya a yayin tarzomar bayan zaben shekara ta 2007 tare kuma da tilastawa wasu dubu 600 yin gudun hijira.

Kenia Wahlen Stim­men­aus­zäh­lung
An tsaurara matakn tsaro a hukumar zaben KenyaHoto: Reuters

Rahotanni na nuni da cewa sama da kuri'u dubu dari 3 ne suka lalace sakamakon gaza bin ka'idojin zaben, wanda kuma hakan ta sanya jama' ke ganin wannan ya faru ne sakamakon gazawar hukumar zaben kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe