Kenyatta ne zababben shugaban kasar Kenya
March 9, 2013Shugaban hukumar zabe ta kasa a Kenya Issack Hassan,ya bayyana dan takara Uhuru Kenyatta, wanda kuma shi ne mataimakin firayiminista a matsayin mutumin da ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata.
Tun can farko dai an sa ran samun sakamakon zaben ne a ranar Laraba, to saidai a dangane da matsalolin kidaya daga nau'rorin da hukumar ke amfani da su, jinkirin ya fara jefa shakku a zukatan magoya bayan bangarorin manyan jam'iyyun siyasar kasar.
Duk da sakamakon wucin gadin da hukumar ta bayyana, dan takara a zaben kuma firaministan kasar Raila Odinga, ya fara kalubalantar sakamakon inda wani mai magana da yawun jam'iyyar yace su dai suna da ja ga sakamakon da aka bayyana ganin cewar an samu kura kurai gurin kidayan kuri'un da aka kada.
Yanzu haka dai Uhuru Kenyatta na fuskantar zargi daga kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifufuka a rikicin da ya barke a lokacin zaben da aka gudanar a kasar a shekara ta 2007 inda a kalla mutane dubu daya da dari biyu suka rasa rayukansu.
Mawallafi : Issoufou Mamane
Edita : Saleh Umar Saleh