1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Khashoggi: Saudiyya ta gargadi kasashe

Ahmed Salisu
February 8, 2019

Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ce Yarima Muhammad Bn Salman ba shi da hannu a kisan dan jaridar nan na kasar Jamal Khashoggi wanda aka hallaka a Turkiyya.

https://p.dw.com/p/3D2Ng
Saudi-Arabien Tabuk Mohammed bin Salman
Hoto: picture-alliance/abaca/Royal Palace/B. Al Jaloud

Adel al-Jubeir da ke zaman karamin ministan harkokin wajen Saudiyya din ya ce duk wani mataki da za a dauka kan Muhammad bin Salman game da kisan na Khashoggi daidai ya ke da takalar kasar da fada wanda in an san farkonsa ba a san karshensa ba.

Ministan ya ambata hakan ne yau lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a birnin Washington na Amirka, inda galibin 'yan majalisar dokokin kasar ke cewar Yarima Bin Salman din ne ke hannu wajen kisan Jamal Khashoggi, batun Saudiyya din ke cewar zargi ne da bai da tushe balle makama.