Mawaka na waken yaki da Coronavirus
March 31, 2020Talla
Wasu mawakan zamani na rere wakokin a shafukan sada zumunta da kafofin yada labarai. Ali Atchibilli shi ne manajan mawakan "Haske Star", da ya fitar da wakar. Irin wanan gudunmawa ta wayar da kan jama'a da zaran irin haka ta samu, nauyi ne da ya rataya a kan kowacce kungiya.
To amma ga Mahaman Mutari Eldezire dan jaridar da ke bibiyar shafukan sada zumunta ko journaliste en ligne dole sakon ya kai ga jama'a. Irin wadannan wakokin wayar da kan jama'ar dai sun mamaye zukatan al'umma, musamamn matasa da ke bibiyar shafukkan sada zumunta