1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kifi ya kashe wani 'dan yawon bude ido a Masar

December 29, 2024

Ma'aikatar muhalli ta Masar ta ce wani gawurtaccen kifi ya kashe wani 'dan yawon bude ido a wajen shakatawa na Marsa Alam da ke gabar tekun Bahar Maliya.

https://p.dw.com/p/4ofFh
Hoto: Wayne Lynch/All Canada Photos/IMAGO

Ma'aikatar muhallin ta ce baya ga mutumin da ya rasa ransa kifin ya kuma jikkata wani 'dan yawon bude ido gudu da ke karbar magani a asibiti.

Karin bayani: Nijar ta dage dokar hana noman tattasai da kamun kifi a Diffa

Hukumomin Masar basu sanar da sunaye da kuma kasashen da mutanen da suka gamu da fushin mari babban kifin a tsibirin Marsa Alam suka fito ba.

Karin bayani: 

Ma'ikatar ta ce lamarin ya faru ne a wani waje da tsibirin wanda kuma aka haramta kai koma a yankin. Makamancin wannan al'amari ya kuma faru a shekara ta 2023, da wani gawurtaccen kifi ya halaka wani 'dan kasar Rasha shiyyar Hurghada da ke Marsa Alam.

Ko a watan Nuwambar 2024, wani jirgin 'yan yawon shakatawa ya kifi a wannan waje da yayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare kuma da wasu mutanen bakwai da suka bace.