1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim Jong Ill na Koriya ta Arewa ya riga mu gidan gaskiya

December 19, 2011

Kafafen yada labarun gwamnatin Koriya ta Arewa sun ba da labarin rasuwar shugaban kasar, Kim Jong Ill bayan da ya yi fama da ciwon zuciya

https://p.dw.com/p/13VLF
A South Korean woman watches TV reporting on North Korean leader Kim Jong Il at a railway station in Seoul, South Korea, Sunday, Oct. 5, 2008. North Korea's state news agency reported a public appearance by reclusive leader Kim for the first time in nearly two months, an absence that prompted speculation he was seriously ill. (AP Photo/Ahn Young-joon)
Marigaya Kim Jong IlHoto: AP

Gidan telebijan Koriya ta Arewa ya ba da sanarwar rasuwar Shugaban kasar Kim Jong Ill. Shugaban na Koriya ta Arewa ya cika ne a lokacin da yake kan hanya a cikin jirgin kasa. Kamfanin dillacin labarun kasar ta Koriya ta Arewa wato KCNA ya ce shugaban yay i fama da ciwon zuciya. A dai shekarar 2008 ne Kim Jong Ill ya kamu da ciwon hawan jini. Tun daga wannan lokaci kuma ya ke ta fama da rashin lafiya. A shekarar 1994 ne marigayijn ya karbi ragamar shugabancin kasar daga hannun mahaifinsa Kim Il Sung . A baya-bayan nan ne kuma ya ba da sanarwar mika wa dansa karami Kim Jong Un ragamar shugabanci.

Kasar ta Koriya ta Arewa ta yi fama da matsananci talauci a karkashin mulkin Kim Jong Ill. Shi dai shugaban ya fuskanci matsin lamba daga kasashen duniya bisa shirinsa na kera makaman kare dangi da masu linzami. A matsayin martaninta ga labarin mutuwar shugaban, Koriya ta Kudu ta ce dakarunta suna cikin shirin ko ta kwana. Tun bayan yakin da suka gwabza daga shekarar 1950 zuwa 1953 ne dai wadannan kasashen ke cikin damarar yaki.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala