Kimanin mutane 3000 sun rasa aiki a Ghana
May 17, 2015Talla
Masu zanga-zangar da suka yi tattaki a babban birnin kasar Accra, sun bayyana cewa dole hukumomi su kawo karshenn matsalar da ake fiskanta da ta shafi karancin wutar lantarki. Daruruwan mutanen da dai sun bayyana takaicinsu, kan cewa duk da keraye-kirayen da jama'a ke yi, kan gwamnati ta dau mataki, amma kawo yanzu shugaba John Mahama kamar ya toshe kunnensa ne. Yanzu haka dai kimanin muta ne 3000 suka rasa ayyukansu bayan da kamfanoni suka rage ayyukansu bisa karancin makashi, abinda ya tilasta musu sallamar ma'aikata.