1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar hare-hare a yankin Sahel

Mohammad Nasiru Awal
December 27, 2019

A tsawon kwanakin bukukuwan Kirismetin an yi ta samun hare-hare da musayar wuta tsakanin masu kaifin kishin addini a kasashen Burkina Faso da Nijar da kuma Mali

https://p.dw.com/p/3VON8
Deutsche Zeitungen nach der Wahl in Hessen
Hoto: DW/H. Flotat-Talon

A wannan mako za mu fara sharhi da labarun jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ta leka kasar Burkina Faso tana mai cewa, bukukuwan Kirismeti cikin zaman makoki. Ta ce fiye da mutane 100 suka rasa rayukansu a wani gumurzu tsakanin sojoji da masu ikirarin jihadi. Wannan na zuwa ne bayan wata ziyarar da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kai yankin yammacin Afirka inda ya jaddada muhimmancin yaki da ta'addanci musamman a kasashen yankin Sahel, yana mai cewa za a shiga sabon salo na yaki da ta'adda. Jaridar ta kara da cewa a tsawon kwanakin bukukuwan Kirismetin an yi ta samun hare-hare da musayar wuta tsakanin masu kaifin kishin addini a kasashen Burkina Faso da Nijar da kuma Mali. Jaridar ta ce yankunan kan iyakoki tsakanin Mali da Burkina Faso da kuma Nijar sun zama tungar kungioyin 'yan ta'addar da a cikin makonnin baya bayan nan suka rika kai jerin hare-hare don nuna karfinsu. Bisa wannan dalili dole kasashen yankin da sauran kasashen duniya su kara himmatuwa su kuma fito da sabbin dubaru matsawar suna su samun nasarar yaki da wannan annoba, inji jaridar.

Symbolbild- Nigera - Militärübung
Jami'an tsaro a yankin SahelHoto: picture-alliance/dpa/P. de Poulpiquet

Za a daina amfani da takardun kudin 'yan mulkin mallaka na Faransa a kasashen Afirka ta Yamma rainon Faransa inji jaridar Neues Deutschland. Ta ce a shekara mai kamawa ta 2020 kasashe takwas na yammacin Afirka da suka taba zama karkashin mulkin mallakar Faransa za su daina amfani da kudin Franc CFA su maye gurbinsa da takardar kudin ECO. Takardar kudin CFA da ake bugawa a Faransa, tun a shekarar 1945 aka kirkiro da ita a kasashen da ke karkashin mulkinm mallkar Faransa, kuma bayan samun 'yancin kansu takardar kudin a hukumance ake amfani a ita a kasashen Benin, Burkina Faso, Cote d'Ivoire, Guinea-Bissau, Mali, Nijar, Senegal da kuma Togo. Kasashen na ajiye kashin 50 cikin 100 nam kudaden ajiyarsu a babban bankin Faransa, don samu garanti daga gwamnatin Paris na daidaita matsayin kudin da na Euro. Jaridar ta ce matakin soke amfani da CFA ya zo ne daidai lokacin da ake kara kyamar Faransa a kasashen da ta raina.

Westafrika CFA-Franc BEAC
Kudin CFA-Franc da za a daina aiki dasuHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kasuwancin kayan gwanjo na kara bunkasa a Afirka, wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürchern Zeitung ta buga tana mai mayar da hankali da tsaffin tufafin daga Turai wanda ta ce kayan da ake ba da su da nufin taimakawa mabukata, amma a Afirka cikinsa ya zama abu mai ribar gaske. Jaridar ta ba da misali da unguwar Adjame da ke birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire inda daruruwan matasa ke harkar ta sayar da tsoffin tufafin daga kasashe masu ci-gaban masana'antu. Sai dai kayan gwanjo wanda akasari kyauta ake bayarwa kadan ne a ciki ke shiga hannun mabukata, domin tun a Turai ake tantance su a saka cikin akwatuna a kuma sayar da su a kasashe masu tasowa, musamman ga kananan 'yan kasuwa.

A karshe sai jaridar Die Tageszeitung wadda ta ce mata a kasar Sudan na alfahari da kuma farin ciki kasancewa zanga-zangar da suka fara a bara ta yi tasiri wajen kifar da gwamnatin Omar al-Bashir. Sai dai har yanzu suna gwagwarmaya a cikin matsin tattalin arziki da kasar ke ciki. Ta ce gwamnatin da aka kafa a watan Agusta karkashin Firaminista Abdalla Hamdok dole ta nemo hanyar magance mawuyacin hali na siyasa da tabarbrewar tattalin arziki da kuma rikice-rikice na masu daukar makami a kasar