1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kisan babban jami'in Hamas na ci gaba da samun martani

Zainab Mohammed Abubakar
January 3, 2024

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Labanon ta bayyana damuwa dangane da yanayin tsaro a kasar, bayan harin da yayi sanadiyyar mataimakin shugaban Hamas Saleh al-Arouri a Beirut.

https://p.dw.com/p/4apUE
Saleh al-ArouriHoto: Ahmed Gamil/AA/picture alliance

Ya kasance jami'in Hamas mafi girma da aka kashe tun bayan barkewar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya a aranar 7 ga watan Oktoba, kisan da ke ci gaba da samun martani mabanbanta.

A cewar jami'in kula da harkokin waje na EU Josep Borrell, dole ne kasashen duniya su samar da hanyar warware rikicin Isra'ila da Hamas saboda bangarorin da ke gaba da juna ba za su iya cimma matsaya ba.

Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Mohammad-Reza Gharaei Ashtiani, ya ce babu shakka kisan da aka yi wa wani babban jigo a kungiyar Hamas a kasar Lebanon zai haifar da sakamako, ya kuma dora alhakin wannan rikici kan Amurka.