1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan jami'in kare haƙƙin 'yan Luwaɗi a Yuganda

January 27, 2011

Ƙasashen duniya sun yi tur da Allah wadai da kisan da aka yi wa jami'in kare haƙƙin 'yan Luwaɗi a ƙasar Yuganda.

https://p.dw.com/p/106FS
Jaridar "Rolling Stone" ta Kampala a ƙasar Yuganda wadda ta wallafa aikata kisa akan 'yan LuwaɗiHoto: AP

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun baiyana matuƙar damuwa game da kashe David Kato jami'i mai fafutukar kare haƙƙin 'yan Luwaɗi a ƙasar Yuganda wanda aka yiwa takakkiya har gidansa dake birnin Kampala aka yi masa dukan kawo wuƙa har sai da ya cika. Binciken farko ya nuna cewa wani mutum ne ya daki jami'in mai shekaru 43 da haihuwa a ka kafin ya tsere. David Kato ya rasu a kan hanya a lokacin da ake shirin kai shi Asibiti. Dama dai ya sha samun barazanar kisa tun bayan da wata mujalla ta wallafa sunan sa tare da hoto inda ta yi kiran aiwatar da kisa akan yan Luwaɗi. Bugu da ƙari jam'in ya yi ƙaurin suna wajen sukar lamirin dokar tsaurara hukunci akan yan Luwaɗi wanda ya haɗa da hukuncin kisa. Ƙasar Uganda dai ta haramta Luwaɗi. Shugaban rundunar 'yan sanda ta ƙasar Kale Kayihura yace kisan da aka yi wa Kato ba shi da nasaba da aikinsa na kare haƙƙin 'yan Luwaɗi.

Ana iya sauraron sautin rahoto akan martanin kungiyoyi da kasashen duniya game da kisan jami'in kare haƙƙin bil Adama a ƙasa.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita: Usman Shehu Usman