1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Shin kudirin MDD mabuɗin ne ga makomar Siriya?

December 27, 2024

MDD ta amince da wani kuduri a 2015 a kan yadda za a kawo karshen yakin a Syria, da ma yadda kasar za ta koma ga tsarin dimukuradiyya. Sai dai abin da ake tambaya a kai a yanzu, shi ne ko kudurin na da wani tasiri.

https://p.dw.com/p/4ocvj
Hoto: David Dee Delgado/REUTERS

 Yayin da al'amura ke sauyawa a Syria, bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a ranar takwas ga wannan wata ana Disamba, kudurin na Majalisar Dinkin Duniya da aka samar a 2015, wani abu ne da ake ganin muhimmancinsa kan makomar kasar a nan gaba. Cikin makon da ya gabata ne aka jiyo Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres na fada a birnin New York, cewa "al'ummar Syria sun shiga wani babi da kuma samun wata dama da bai dace a ce sun yi asararta ba. Dama ce da ta kamata ta tafi da kudurin kwamitin sulhu na Resolution 2254" a cewar Mr. Guterres. Wasu ma daga cikin manyan jami'an diflomasiyyar duniya, irin su Antony Blinken na Amurka da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, duk sun yi magana shigen ta jagoran na  MDDa kan Siriya.

Abu Mohammad al-Julani sabon shugaban Siriya
Abu Mohammad al-JulaniHoto: Orient News TV Handout/dpa/picture alliance

A makon jiya kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da sanarwar da ke na'am da matsayin da Antonio Guterres ya bayyana, duk kuwa da cewa wasu mambobinsa na da bambancin ra'ayi a game da batutuwan da suka shafi Siriya.Kasar Rasha, guda daga cikin mambobin kwamitin na sulhu da ke da dadaddiyar alaka da gwamnatin Bashar al Assad da aka kifar, na da hannu cikin yakin basasar Siriyar, ta hau kujerar na ki a lokuta da dama a kan batutuwa masu nasaba da tsohuwar gwamnatin ta Assad.Rashar ta sha bijire wa batutuwa masu nasaba da bincike rusasshiyar  gwamnatin musamman amfani da sinadarai masu guba da sauran muyagun makamai. Kudurin na MDD dai kuduri ne da ya samu rinjaye a 2015 lokacin da zubar da jini ya yi matukar muni a yakin Siriya, inda tsarinsa ya nuna kokari na ganin an tsagaita bude wuta.Sannan a kawo karshen mulkin gidansu su Assad da ke jagotrantar kasar tun a shekarar 1971 da aka bayyana da kama-karya, domin girka dimukuradiyya. A shekara ta 2012 ne dai batun kudurin ya taso, bayan wata sanarwar bayan taron da aka yi a birnin Geneva na kasar Switzerland, taron da ya hada ministocin harkokin wajen kasashen Tarayyar Turai da Amurka da Burtaniya da Turkiyya da China da ma Rasha, amma kuma babu wani wakilci daga Siriya.

Syrien Konflikt
Hoto: Louai Beshara/AFP

Wasu dai daga cikin abubuwan da kudurin ya kunsa dai ba za su iya amfani ba a yanzu da sabon jagoranci da ke a Syria, musamman batun karba-karba na mulki karkashin Assad. Shi ma jagoran gwmanatin Siriya na yanzu, Ahmad al-Shar'i ya yi bayani kan shurewar wasu daga cikin kudurin. A karshen makon jiya ma jagoran tawagar Majalaisar Dinkin Duniya a Siriya, Geir Pederson ya fada a birnin Damascus cewar jagoran gwamnati al-Shara'I ya nuna bukatar sake inganta kudurin ta yadda zai iya dacewa da halin da ake ciki a kasar a yanzu. To sai dai kuma ministocin kasashen Masar da Saudiyya  da Jordan da Iraki da Qatar da suka hadu a birnin Aqadan a Jordan sun ba da shawarar Siriya ta yi amfani da abin da kwamitin sulhun na MDD ya cimma a  2015.