Kofi Annan ya kammala ziyara sa a Siriya
March 11, 2012Manzon na Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar ƙasashen larabawa Kofi Annan ya ce ya na da kyaukyawan fatan cewar za a samu masalha a rikicin ƙasar Siriyar ;tsohon babban sakataran na MDD ya baiyana haka ne a wani taron manema labarai da ya yi bayan da ya gana a karo na biyu da shugaba Bashar al Assad.
Wanda ya ce ya gabatar masa da nagartatun shawarwari na samun mafita ;amma du da haka ya ce nauyi da aka ɗora masa na samar da zaman lafiya a Siriya abi ne da ke da wuya.''ya ce a kwai wahala amma ba zamu yanke ƙauna ba, muna sa ran za a cimma nasara ;ya ce kusan dukanin jama'a da na gana da su yan Siriyar a wannan yar guntuar ziyara kowa ne na fatan ganin an sake dawo da zaman lafiya''.Mista Annan ya ce shawarwarin da suka yi da shugaba Assad sun maida hankali ne akan dakatar da tashin hankalin da kisan jama'ar, tare da ba da damar isar da kayan agaji da kuma soma gudanar da tattaunawa da yan adawar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi