1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kofi Annan zai shiga tsakani a rikicin siyasar ƙasar Kenya

January 11, 2008
https://p.dw.com/p/Co3c

Bayan rugujewar ƙoƙarin da ƙungiyar tarayyar Afirka AU ta yi na shiga tsakani don kawo karshen takaddamar da ake yi dangane da zaben ƙasar Kenya, yanzu tsohon sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan zai karɓi ragamar yin sulhu. A jiya alhamis shugaban Kenya Mwai Kibaki da jagoran ´yan adawa Raila Odinga sun amince da mista Annan ya yi sulhu. Shugaban ƙasar Ghana kuma shugaban ƙungiyar AU a yanzu John Kufour ya ba da sanarwar cewa kwanaki biyu da ya shafe yana ƙoƙarin yin sulhu ba su haifar da ɗa mai ido ba. Ƙasar Kenya wadda ke yankin gabashin Afirka tana fama da tashe tashen hankula tun bayan zaben shugagan kasar da ya gudana a cikin watan Disamba, wanda Kibaki ya yi nasara amma ´yan adawa ke zargin an tabka maguɗin zabe. Akalla mutane 600 aka kashe sannan wasu dubu 250 suka tsere daga gidajensu sakamakon hargitsin da ya ɓarke bayan zaɓen na ranar 27 ga watan Disamba.