1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tattauna hanyar sulhunta rikicin kogin Nilu

Abdoulaye Mamane Amadou SB
November 1, 2020

Kasashen Masar Sudan da Ethopiya sun sake komawa kan batun tattaunawar rikicin kogin Nilu watanni uku bayan da aka dakatar da duk wata tattaunawa tsakanin kasashen bayan Habasha ta kafa madatsar ruwa.

https://p.dw.com/p/3kjeC
Äthiopien Grand Renaissance Staudamm
Hoto: Reuters/T. Negeri

Za a shafe tsawon mako guda ana tattaunawar kafin cimma wata matsaya kan batun a cewar ministan albarkatun ruwan Ethopiya a shafinsa na twitter, kana kuma taron da ke gudana ta hanyar bidiyo na tafiya ne karkashen jagorancin Kungiyar Tarayyar Afirka, mai samun rakiyar EU da Amirka da asusun ba da lamuni na duniya IMF da ma Bankin Duniya.

A can baya dai an fuskanci takon saka tsakanin kasashen tun bayan da Habasha ta gina madatsar ruwa a yankin domin samar da shirinta na wutar lantarki mafi girma a nahiyar Afirka, lamarin da ya kai kasar Masar ga shigar da kara a gaban kwamitin sulhu na MDD a cikin watan yunin da yagabata.