1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin dakile matsalar abinci a Nijar

Mahaman Kanta/ LMJOctober 16, 2015

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar da tallafin kungiyoyin kasa da kasa na daukar matakan tallafawa manoman kasar domin yaki da karancin abinci.

https://p.dw.com/p/1GpbV
Dürre im Niger
Hoto: picture-alliance/dpa

Ministan kula da ayyukan gona a Jamhuriyar Nijar da wakilan kungiyoyin bada agaji na duniya da suka hada da FAO da UNDP da PAM sun bayyana mahimmancin kawar da matsalar abinci. Jamhuriyar Nijar dai na fuskantar matsalar karancin ruwan sama a wasu lokutan wanda hakan ke janyo karancin abinci a kasar. Sai dai al'ummar kasar sun dukufa sosai wajen noman rani wanda hakan ya taimaka gaya wajen shawo kan matsalar karancin abincin da kasar ke fuskanta.

Rahotannin sun nunar da cewa Jamhuriyar ta Nijar ta rage kaso 50 cikin 100 na matsalar abincin da take fuskanta wanda hakan ya sanya ta taka rawar gani wajen cimma muradan ci-gaban karni na Majalisar Dinkin Duniya a wannan fannin. Kungiyoyin kasa da kasa ma dai na ba yar da nasu tallafin domin shawo kan wannan matsalar inda kungiyar kula da abinci ta Mjalisar Dinkin Duniya (FAO) ta ba da tallafin injinan ban ruwa da ke amfani da hasken rana ga manoman wadanda za su tallafa musu wajen janyo ruwan daga fadamu zuwa gonakinsu.

Ita ma dai gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar a nata bangaren ta dauki matakan rabawa al'umma abinci da kuma tallafa musu ta hanyar wuce musu gaba wajen neman basussukan gudanar da ayyukan gonakinsu a bankuna dama shirin nan da ta bullo da shi na dan kasa ya ci da dankasa duk dai da nufin tallafawa manoman.