1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin dakile ta'addanci a Kenya

December 19, 2014

Majalisar dokokin kasar Kenya ta kada kuri'ar amincewa da dokar yaki da ta'addanci a kasar da ta tanadi hukunci mai tsauri ga wanda aka samu da aikata laifukan ta'addancin.

https://p.dw.com/p/1E7GH
Hoto: Reuters/T. Mukoya

An dai baiwa hammata iska gabanin amincewa da dokar tsakanin 'ya'yan jami'iyyar adawa da kuma na jam'iyya mai mulki a majalisar dokokin ksar ta Kenya. Sabuwar dokar dai ta amince da gwamnati ta murkushe duk wasu mutane da ake zargin 'yan ta'adda ne tare kuma da rage 'yancin samun bayanai ga 'yan jaridu. Mahukuntan kasar ta Kenya da a 'yan kwanakin nan ta sha fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyar al-Shabaabebab ta Somaliya, sun ce dokar ta zamo wajibi domin dakile ayyukan 'yan ta'adda a kasar. Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma 'yan adawa suna ganin an take 'yancin al'umma a wasu sassa na dokar. A yanzu dai jami'an tsaron kasar za su iya tsare duk wani da ake zargin dan ta'adda ne na kusan tsahon shekara guda sabanin kwanaki 90 din da ake tsare su a yanzu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu