Kokarin gano mahara a Kenya
December 15, 2013Talla
'Yan sandan kasar Kenya sun kaddamar da binciken hari kan motar safa da ya yi sanadiyar hallaka mutane shida, yayin da wasu 30 suka samu raunika. Kuma hari na baya-baya cikin bukukuwan cika shekaru 50 da samun 'yanci da aka gudanar a kasar.
Wasu rahotannin sun ce an yi amfani da gurneti wajen kai harin, kuma kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin wannan hari.
Ana danganta yawan hare-haren da ake kai wa kasar ta Kenya, da kungiyar tsageru ta al-Shaabab mai alaka da al-Qaeda da ke Somaliya, wadda ita da kanta sau da yawa ta kan fito fili da dauki alhakin hare-haren. Kasar ta Kenya ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen gabashin Afirka.
Mawallafi : Suleiman Babayo
Edita : Saleh Umar Saleh