Wasnnin domin hadin kai a Najeriya
June 10, 2015Wasan kwallan kafa da na tseren keke da na takalmin taya da gudun dogon zango “wato Marathon” tare da sauran wasanni na daga cikin jerin wasanin motsa jiki da malaman addinai a Najeriya suka bullo da shi a wannan lokacin. An dai shirya wadannnan wasannin ne domin hadakan daukacin matasan kasar, da nufin kawo karshen rigingimun da suka jibanci na siyasa da kabilanci da na addini da ke addabar kasar wanda kuma ke janyo asarar rayuka da miliyoyin dukiya. Pastor Yohanna Buru na Cocin Christ Evengelical shine ya shirya wanna wasa kuma ya ce sun dade suna shirye ire-iren wadannan wasani domin kawo karshen zaman doya da manja da ke aukuwa tsakanin matasa Musulmai da Kirista. Ya ce a kwanakin baya sun shirya taruka daban-daban, sai dai sun lura cewa, bai haifar da wani da mai ido ba, a saboda haka ne suka bullo da wasu sababbin dabarun kawo zaman lafiya tsakanin mabiya addinan. Babu shakka wannan sabon salun hada kan matasa ta hanyar wasanin motsa jiki akwai nasarori da dama da aka samu. Malam Abdulrahman Mohammad Bichi daya daga cikin malaman addinin Musulunci da ke fafatukar tabbatar da dorewar zaman lafiya a cikin kasar ya ce malaman addinin Musulunci da na Kirista na zaman fahimtar juna akai-akai domin kara samun kyakkyawar dangantaka da kuma alaka.