Fara tattaunawa domin kawo karshen zubar da jini a Yemen
June 15, 2015Talla
A yayin da yake kaddamar da zaman tattaunawar sulhun a birnin Geneva na kasar Switzerland, Ban ya bukaci da a tsagaita wuta domin samun damar kai kayan agaji ga al'ummar da suka shiga halin tasku sakamakon hare-haren jiragen yakin rundunar taron dangi da Saudiyya ke jagorantar kaiwa a kasar. Sai dai a nasa bangaren ministan harkokin kasashen ketare na Yemen din Reyad Yassin Abdulla ya ce bai ga alamun hakan za ta samu ba, yana mai cewa tilas ne 'yan Houthi su fice daga biranen da suka kwace iko da su a kasar kafin a yi batun tsagaita wutar. Sama da mutane 2,600 ne dai aka tabbatar da cewa sun hallaka tun bayan da Saudiyya ta kaddamar da jagorantar yin ruwan bama-bamai a Yemen din.