Kokarin Koriya ta Arewa na kare kanta
April 9, 2015Talla
A wani rahoto da aka gabatar gaban majalisar dokokin kasar, Koriya ta Arewan ta ce abinda ta sanya gaba shi ne ta ga ta magance masassarar da tattalin arzikinta ke fuskanta.
Sai da a hannu guda kamfanin dillancin labarai na kasar na KCNA ya rawaito wani kusa a gwamnatin kasar na cewar muhimmancin daidaita al'amura na tattalin arzikin kasar na kan doro guda da kare kasar daga duka wata barazana.
Koriya ta Arewa din dai ta ce za ta kashe akalla kashi 15 cikin 100 na kasafin kudinta na bana kan harkokin da suka danganci tsaro kamar yadda ta yi a shekarar da ta gabata.