1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin sake gina Somaliya

September 27, 2017

Kasar Somaliya ta sami kanta cikin tsaka mai wuya tsakanin kokarin sake gina da kasar da kuma yaki da 'yan ta'adda. Kasashen duniya dai na kokarin hada hannu domin taimaka mata shawo kan matsalar.

https://p.dw.com/p/2kpeC
Somalia Mogadischu | Flüchtlingsgruppe aus Bariire
Hoto: DW/S. Petersmann

A kasar Somaliya dai bayan jirage masu sarrafa kansu da ake kira Drones a turance, Amirka ta kuma kara yawan sojojinta na kundunbala a cikin kasar domin yaki da yan gwagwarmayar Al Shabaab. Wannan lamari dai ya jefa kokarin sake gina kasar cikin babban hadari.

A garin Bariire da ke kudancin Somaliyar babu abin da yan gudun hijira suke tattaunawa akai kamar yawan sojojin kasashen ketare da harbe harben bidigogi da fashewar bama bamai da kuma hare hare ta sama da ke faruwa. A wasu lokuta ma dai rayuwa da harkokin yau da kullum kan kasance cikin kunci da alhini har tsawon kwanaki. Jama'a na cikin zullumi da fargaba ta kowane bangare kamar yadda Mariam wata wadda aka kashe maigidanta ta bayyana.

Somalia Mogadischu | Flüchtlingslager, geflohene Witwe Faduma
Hoto: DW/S. Petersmann

A bayan da aka kawo karshen yakin Bariire ne Mariam ta gano gawar mijinta jina jina da harbin harsashi a jikinsa. 'Ya'yanta bakwai sun yi rashin mahaifinsu. Shin wane ne ya yi masa wannan harbi kuma tun a wani lokaci aka aikata wannan danyen aiki? Abin da ba ta sani ba ke nan.

A yanzu dai Mariam da sauran mutanen da suka tsere suna zaune ne a wani sansani a Mogadishu babban birnin Somaliya. Su dai manoma ne. Garin Bariire yana yankin Shabelle na kudancin Somaliya, yana kuma tazarar kilo-mita 60 daga Mogadishu.

Kafin wannan lokacin dai Bariire nan ne matattarar 'yan kungiyar Al-Shabaab mai gwagwarmaya da makamai wadda kuma ta sanar da yin mubaya'a ga kungiyar Alka'ida, ta na mai ikrarin yaki domin kafa daular musulunci. Sai dai a ranar 20 ga watan Augusta sojojin kungiyar gamaiyar Afirka AU tare da sojojin Somaliya sun yi nasarar kwace garin na Bariire. Kungiyar ta AU ta girke sojoji 22,000 a Somaliya wadanda ke fafatawa da 'yan Al Shabaab.

Somalia Mogadischu | Flüchtlingsunterkunft
Hoto: DW/S. Petersmann

Somaliya ta fada halin yaki da tashin hankali ne tun a shekarar 1991. Gwamnatin ta kasa katabus yayin da manyan hauloli suka karbe ragamar iko a kasar.

A yanzu dai ana kokarin sake gina kasar tare da taimakon kasashen duniya.  A watan Disambar bara aka kafa sabuwar majalisar dokoki yayin da a watan Fabrairun wannan shekarar kuma aka rantsar da sabon shugaban kasar. A dukkan zabbukan biyu dai manyan haulolin Somaliyar sun yi ta gwagwarmaya kan madafan iko da kudi da suka rika sauya hannu. To sai dai manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Somaliya Michael Keating ya shaidawa Deutsche Welle cewa an sami cigaba mai ma'ana.

Somalia Mogadischu | Altstadtstrand
Hoto: DW/S. Petersmann

A waje guda dai shugaban kasar Mohammed Abdullahi Mohammed ya sami amincewar al'umma. Ya kuma kudiri aniyar mayar da 'yan gudun hijira. Bugu da kari shugaban kasar yana da shidar dan kasa na Amirka. A saboda haka yake neman karin goyon bayanta ta fuskar tsaro da juba jari da kuma samun tallafin kudi ga gwamnatinsa.

A babban birnin kasar dai ayyukan gine-gine na ta gudana, ana kuma gina sabbin tituna. Harkoki sun kankama a wuraren shan shayi da kantuna. Yayin da 'yan kasashen waje da sauran masu ba da tallafi ke ci gaba da kai ziyara kasar. Ana kuma gina ofisoshin jakadanci. To amma galibin 'yan kasashen waje na zama a wuraren da aka kange da katuwar katanga da kuma filin jirgin sama wanda aka kange domin kariya ga harin bama-bamai na 'yan kunar bakin wake. A daya hannun kuma ana samun matsalar garkuwa da mutane a kullum a kasar ta Somaliya. Duk wadannan dai sun kasance manyan kalubale wajen magance tarin matsalolin da suka yi wa kasar dabaibayi.