Kokarin Sin da Japan wajen warware rikicin nuclearn koriya ta arewa
November 18, 2006Primenistan Japan Shinzo Abe da shugaba Hu Jintao na kasar Sin,sunyi alkawrin tursasawa gwamnatin koriya ta arewa ta koma teburin tattaunawar nan daya kunshi kasashe 6,akan shirin nuclearnta,tare kuma da haramtawa Japan din mallakar makaman nuclear.Ayau din ne kuma premiern japan din yayi ganawarsa ta farko da shugaba Georgve W Bush ,a bayan fagen taron kasashen yankin Facifik dake gudana a birnin Hanoi din kasar Vietnam.Jamian Japan dai sun ruwaito cewa tattaunawar magabatan biyu ya mayar da hankali ne,wajen kokarin jan hankalin Koriya ta arewa wajen watsi da makamanta na Nuclear.A ranar 9 ga watan Oktoban daya gabata nedai koriya ta arewan ta gudanar da gwajin makamin nuclearnta na farko,wanda kuma a sanadiyyarsa ne Japan ta yanke dukkan huldodin kasuwanci da ita.