1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NIjar: Bazoum ya gana da malamai

Salissou Boukari
May 11, 2021

A wani mataki na shawo kan matsalar tabarbarewar harkokin ilimi na tsawon shekaru, shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya yi wata ganawa da kungiyoyin malaman makaranta.

https://p.dw.com/p/3tG3a
Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum
Hoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

Ganawa wadda ita ce irinta ta farko, ta yi nuni da irin kalaman da shugaban kasar ya yi tun a lokacin yana neman shugabancin kasar ta Nijar, inda ya ce a matsayinsa na malamin makaranta batun tabarbarewar ilimi a wannan a Nijar na ci masa tuwo a kwarya, wanda yake fatan da zarar ya samu shugabancin kasar ya dauki matakan gyara.

To za a iya cewa ganawa ta keke da keke da shugaban ya yi da wadannan kungiyoyi da kuma abubuwan da aka tattauna a kansu na nunin cewa lalle da alama kwalliya ka iya biyan kudin sabulu idan har aka tafi a haka wajen samun fahimtar juna tsakanin bangarorin da a waccan gwamnati da ta shude, ba a yi ga-maciji da juna.

Da yake magana yayin soma tattaunawar shugaban kasa Mohamed Bazoum ya sanar da dalillansa na yin wannan ganawa:

Schule in Niamey
Dalibai a cikin aji a YamaiHoto: DW/A. Mamane Amadou

"Na kudiri aniyar yin wannan ganawa tare da ku shugabannin kungiyoyin malaman makarantun boko domin na jaddada muku matakin da tuni muka soma magana a kanshi, shine na neman hanyoyin inganta harkokin ilimi a wannan kasa tamu, ta yadda gaba dayanmu zamu yi aiki wajen magance matsalolin da ke hana ruwa gudu. Na yi imanin cewa a fannin bincike da kididdiga na wadannan matsaloli, nasan zamu fahimci juna sosai. Mafi mahimmanci daga cikin wannan aniya tamu shine maganin da zamu kawo wa ciwon da tsarin harkokin ilimin ke fuskanta a wannan kasa ta Nijar."

Matakin dai zai shafi tsarin karatu na Firamare, sakandire da kuma Jami'a, sannan a hanhu daya za a duba yadda za a inganta bayar da horo a makarantu koyon ayyukan hannu ta yadda ilimin da ake bayarwa zai amfani mai shi ya kuma amfani kasa. Sai dai su da kansu shugabannin kungiyoyin Maluman makarantun da suka halarci wannan tattaunawa, sun ce lalle sun ga alamar sauyi domin maimakon irin kwamiti da ake kafawa na ministoci da shugabannin kungiyoyi a nan shugaban kasa da kanshi ne ya gana da su domin daukan matakan tare.

A fannin ilimi na kananan makarantu shugaban na son saka tsari na makarantar kwana a wasu yankuna a matsayin gwaji ta yadda 'ya'yan talakawa za su rinka karatunsu ba tare da wata fargaba ta rashin masauki ko abninci ba, wanda kuma hakan ake ganin zai kara bunkasa karatun diya mata a wannan kasa da yara yan mata suka gwamnace zuwa talla maimakon makarantu, amma kuma cimma dukannin wannan buri sai da malumai masu inganci da kuzari da ke aikinsu cikin kwarewa da nuna son kasa.

Unruhen in Niger April 2014
Lokacin da dalibai ke zanga zanga a 2014Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Sai dai da alama Shugaba Bazoum bai yi wa shugabannin kungiyoyin malaman makarantun kalamai na ganin idanu ba, inda kai tsaye abubuwan da ba zai iya yinsu ba ya sanar da su cewa gaskiya wannan ba zai dawo kansu ba, kamar misali malamai da aka kor ata sabili da rashin kwarewa bayan jarabawar da aka yi, da kuma wani batun da shi ma tuni kotu ta bai wa maluman rashin gaskiya sai shugaban ya ce ba zai tayar da wannan magana ba. Wannan shine irin karin maganar nan da masu gaskiya ke cewa mana karya don a soni.