1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin warware rikicin nukiliyar kasar koriya ta arewa

December 18, 2006
https://p.dw.com/p/BuXO

Wakilin kasar Amurka a tattaunawar kasashe shidda, a game da rikicin nukiliyar kasar Koriya ta arewa, wato Christopher Hill ya bukaci Koriya ta arewa data mayar da hankali kann kawo karshen aniyar ta na mallakar makamin Atom.

Kafafen yada labarai dai sun rawaito Mr Hill na fadin hakan ne jim kadan bayan isar sa birnin Beijin, don ci gaba da tattaunawar kasashe shidan.

Tattaunawar wacce ta samu tsaiko na wasu watanni, a yanzu haka bayanai sun shaidar da cewa zata ci gaba kamar yadda aka tsara a tsakanin wakilan kasashen Amurka da Japan da Russia da kasar Sin da kuma Koriya ta kudu da kuma ta arewa,.

Wannan dai tattaunawa a cewar rahotanni tazo ne bayan watanni biyu da kasar koriya ta arewa tayi gwajin makamin ta na nukiliya.