1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin yin sulhu a rikicin Siriya

January 19, 2014

'Yan adawar Siriya sun amince su halarci taron sulhun da za a yi kan rikicin kasar da ya shiga shekararsa ta uku.

https://p.dw.com/p/1AtRc
Hoto: picture-alliance/dpa

Kungiyar 'yan adawar Siriya da ke gudun hijira ta ce za ta halarci taron da za a yi na kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar wanda ake sa ran gudanarwa nan da 'yan kwanaki a birnin Geneva na kasar Switzerland.

A ranar Asabar kungiyar ta amince da halartar toron bayan kuri'ar da ta kada kan wannan batun, lamarin da ya sanya ake ganin zai zaburar da kasashen ketare su shiga a dama da su a taron don kawo karshen yakin basasar Siriyan da ya shiga shekararsa ta uku.

Da ya ke tsokaci kan wannan matakin da 'yan adawar suka dauka, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi maraba da wannan shawarar da suka yanke yayin da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce 'yan adawar ta Siriya sun yi namijin kokari wajen amincewa su hau kan teburin sulhu don kawo karshen zub da jinin da ake a kasarsu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal