Koma baya kan warware rikicin Siriya
May 1, 2013Talla
Guda daga cikin jakadun kasashen labarawa a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ne ya tabbatar da hakan a wata hira da yi da kamfanin dillacin labarai na AFP inda ya ce Mr. Brahimi ya shaida mu su cewar zai yi murabus kasancewar babu alamar kaiwa ga warware rikicin kasar duba da yadda kan kasashen duniya ya rabu dangane da rikicin.
Baya ga wannan matsalar a hannu guda 'yan tawayen na Siriya sun zargi Brahimi da gaza yin daidaito wajen warware rikicin yayin da gwmantin Assad a nata bangaren a makon da ya gabata ta ce ba za ta sake tattaunawa da shi ba dangane da sasasanta bangarorin biyu.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar