Korafe-korafe dangane da nadin ministocin Tibunu
August 17, 2023Ma'aikatun tattali na arziki ya zuwa ga ma'adinai na karkashin kasa da ruwaye da sadarwa da daukacin harkar man fetur duk suna karkashin moinistoci na kudancin tarrayar Najeriya, a yayin da batun tsaro ya tashi da ministoci har guda biyu duk na Arewa baya ga ministan 'yan sanda da minitan cikin gida da ma masharwacin tsaron kasar. Dr Yahuza Getso da ke zaman kwarrare kantsaron ya ce tsarin gwamnatin Tinubu na zaman babban sako ga sashen arewacin kasar.
Wani tsarin da ya kara fitowa fili daga zabin na Tinubu na zaman yadda aka rika hada manya da kananan ministocin na ma'aikatu guda daga sashen arewacin kasar. Alal misali, daukacin ministocin ilimi sun fito daga Arewa ba ya ga ma'aikatar gida da raya birane. Sannan na tsaron da ministocin albarkatun ruwa ma sun zama wakilan Arewa.
An dauko tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike tare da ba shi ministan Abuja. A karon farko, wani mutumin kudancin kasar zai jagoranci ma'aikatar ta Abuja mai tasiri tun bayan Mabolaji Ajose adegun da ya zamo ministan farko a cikin birnin a lokacin da aka kafa shi. Shugaban a karon farko na lokaci mai nisa ya dauki fararen hula ya kuma mika musu batun tsaron kasar da ke fuskantar karuwar rigingimun rashin tsaron. Saii dai Dr Husaini Tukur Hasan ya ce dabarun Tinubu ba su saba da tsohuwar al'adar tarrayar Najeriyar ba.
Babban fata da buri na zaman iya kaiwa ga sake farfado da tattalin arzikin Najeriya da ke cikin laka, ko bayan samar da tsaron da ke nuna alamun dada lalacewa a yanzu. Sai dai Senata Umar Tsauri dake zaman jigo a jam'iyyar PDP ta adawa ya ce da kamar wuya a iya tatse ruwa ga gwamnatin da ke fadin a sake lale.
Bayan jira na kwanaki 100, hankali 'yan Najeriya daga dukkan alamu na shiri karkata zuwa ga shekara ta farko ta gwamnatin Tinubu da ta fara da zunguro sama da kara, kuma ta ce tana da burin sauya rayuwa a lokacin kalilan.