Koriya ta arewa na bikin shekaru 100 da haihuwar shugabanta na farko
April 15, 2012Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un ya yi jawabinsa na farko ga al'umar kasar wanda aka yada ta akwatunan talabijin a yayin da kasar ke bikin cika shekaru 100 na ranar haihuwar Kim Il Sung wanda ya jagoranci kwato yancin kasar. Kim Jong Un wanda ya gabatar da jawabinsa a gaban dubban daruruwan jama'a yace sojoji za su cigaba da jan ragamar kasar kamar yadda ya kasance a zamanin mahaifinsa wanda ya rasu a watan Disambar bara. Ko da yake kasar ta Koriya ta arewa bata yi nasara ba wajen harba rokanta mai cin dogon zango a makon da ya gabata, jawabin shugaban wani yunkuri ne na karfin hali domin nuna yana da cikakken ikon ragamar kasar a hannunsa. Kim Jong Un yace lokaci ya wuce da za'a yi amfani da makamin nukiliya don yiwa kasar barazana.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman