Koriya ta arewa na shirin gwajin makamin nukiliya
October 3, 2006Talla
Mahukuntan koriya ta arewa sun sanar da matakin gwada makamin su na nukiliya, a wani mataki na tauna tsakuwa don aya taji tsoro.
Sanarwar data fito daga ma´aikatar harkokin wajen kasar ta ci gaba da cewa, kokarin daukar wannan mataki, yazo ne bisa irin matsin lamba da kasar take fuskanta daga kasar Amurka.
Ya zuwa yanzu dai tuni Japan tayi Allah wadai da wannan aniya da kasar ta koriya ta arewa ke son dauka, da cewa zata mayar da martanin daya dace nan bada dadewa ba.