Koriya ta Arewa na yin tunanin watsi da shirinta na nukiliya
May 8, 2016Talla
Kim Jong Um wanda ke yin magama a wajen babban taro na jam'iyyar da ke yin mulki ta ma'aikata watau PTC wanda rabon da a yi irinsa tun a shekara ta 1980. Ya ce ƙasarsa za ta taimaka wajen hana yaɗuwar makaman nukiliya a duniya, tare da neman sake daidaita hulɗa da Amirka da kuma Koriya ta Kudu.
A baya dai Koriya ta Arewa ta shan yi barazanar cewar za ta kai wa Amirka da Koriya ta Kudu hare-hare na makaman Nukiliya, tare kuma da ƙaddamar gwaje