Koriya Ta Arewa ta amince da yarjejeniyar rufe tashoshin nukiliyar ta
October 3, 2007Talla
Shugaban Amirka GWB yayi maraba da yarjejeniyar da aka cimma wadda a karkashin ta KTA zata rufe dukkan tashoshinta na nukiliya kafin karshen wannan shekara. A karshen mako aka tsara ka´idojin yarjejeniyar a gun wani taro na kasashen nan 6 da suka hada da China, KTK da TA, Japan, Rasha da kuma Amirka a birnin Beijing. Idan dukkan kasashen 6 suka amince da yarjejeniyar kuma KTA ta aiwatar da ita to wannan yarjejeniya zata wani gagarumin ci-gaba da burin Amirka na shawo kan KTA ta yi watsi da shirin ta na nukiliya. Za´a saka ma kasar da jerin taimakon tattalin arziki.