Koriya ta Arewa ta amince ta rufe tashar nukiliyar Yongbyon
June 23, 2007Talla
Amirka da KTA sun cimma yarjejeniya kan rufe tashar sarrafa sinadarin plutonium na gwamnatin birnin Pyongyang a cikin makonni 3 masu zuwa. Babban mai shiga tsakani na Amirka Christopher Hill ya ce ana iya fara zagaye na gaba na tattaunawa game da shirin nukiliyar KTA a farkon watan yuli wato gabanin a kammala aikin rufe tashar nukiliya ta Yongbyon.
O-Ton Hill:
“Muna sa rai za´a rufe tashar Yongbyon bayan an cimma wata yarjejeniya tsakanin KTA da hukumar makamashi ta MDD IAEA akan sa ido ga aikin rufe wannan tasha. Ana iya yin haka a cikin makonni 3. Ba zan iya ba da takamammen lokaci ba amma haka zai auku a cikin wannan wa´adi.”
A ranar talata mai zuwa dai ne sifetocin hukumar IAEA zasu isa a kasar ta KTA inda zasu fara tattaunawa game da rufe tashar nukiliyar ta Yongbyon.