Koriya ta arewa ta bukaci dage dukkanin takunkumi da aka lakaba mata
December 18, 2006Talla
Koriya ta arewa ta bukaci a dage dukkanin takunkumi dake kanta kafin ta amince dakatar da gwaje gwajenta na nukiliya,yayinda kasar Amurka kuma tace hakurinta ya kusa karewa game da jagircewa da Pyonyang takeyi akan wannan batu.
Koriya ta arewan wajen bude taron kasashe 6 masu tattaunawa kann shirin nata na nukiliya ta mika wasu kaidoji da tace muddin aka bi zata dakatar da shirinta na nukiliya,cikinsu kuwa har da batun daga dukkanin takunkmi da Amurka da MDD suka lakaba mata.
Sai dai tunda farko jakadan Amurka a taron Christopher Hill yace dage takunkumin ya dogara ne kann dakatar da shirin nukiliyar na Koriya ta arewa.