1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya data dakatar da dukkan agaji da take bata

Hauwa Abubakar AjejeSeptember 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvZR
shugaba kim jong il na koriya ta arewa
shugaba kim jong il na koriya ta arewaHoto: AP

Koriya ta Arewan a yau tace ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen dukkan taimakon abinci da take bata,saboda a cewarta kasar Amurka ta sanya siyasa cikin batun baiwa koriyan agajin abinci hakazalika kuma,Koriyan ta rigaya ta inganta hanyoyin samarda abincinta.

Mataimakin ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa,Choe Su Hon ya baiyanawa manema labarai cewa,ya bukaci sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya wajen ganawarsu ajiya cewa,Koriya ta samu kyakyawar anfanin gona a bana daya sassauta matasalar abinci a kasar,saboda haka sun bukaci shi daya kawo karshen agajin abinci ga kasar daga nan zuwa karshen wannan shekara,musamman ma ganin yadda kasar Amurka take danganta batun da batun kare hakkin bil adama.

Wani kakakin maaikatar harkokin wajen Amurkan ya karyata cewa Amurkan tana neman siyasantar da batun agajin zuwa Koriya.

Yace shawarar Amurkan ta dogara ne kan batutuwa uku da suka hada bukatar kasar da abin ya shafa,da bukatun wasu kasashen kuma hakazalika da tabbatar da cewa agajin ya kai ga wadanda suke bukata.

Kodayake mataimakin ministan na Koriya yace kasarsa zata ci gaba da neman taimakon raya kasar daga kasahen duniya.

Wannan mataki da Koriya ta Arewan ta dauka zai kawo matasala ga makomar hukumar agajin abinci mafi girma a duniya wadda take hankoron ciyarda talakawan Koriya ta Arewa su miliyan 6 da rabi cikin jamaar kasar miliyan 22 da rabi.

Shirin na samarda abinci na Majalisar Dinkin Duniya,a wani rahotonsa na baya bayan nan,ya baiyana cewa duk da cewa Koriya ta Arewa ta samu anfanin gona a bana,har yanzu kasar tana bukatar taimakon abinci daga waje,wadda rahoton yace ba tare da wannan taimako ba,Koriya ta Arewan ba zata iya ciyarda miliyoyn yara,da mata masu juna biyu,tsoffi,da talakawan kasar.

Yayinda kuma Koriya ta Kudu take kara taimakon abinci ga Koriya ta Arewan,maaikatan agaji sunce ba a rabar da shi yadda ya kamata.

Shirin samarda abinci na duniya ya kai ziyara sau 5000 zuwa 6000 zuwa Koriya ta Arewan domin ganin cewa abincin ya kai ga wadanda suke bukata.

Cikin wannan shekarar kadai,shirin samarda abincin ya bada agajin abincin ga Koriya ta Arewa fiye da ton dubu dari biyu da sabain,kuma tana shirin kara ton dubu 33 kafin karshen wannan shekarar.

Hakazalika koriya ta Arewan ta karbi agajin magunguna da alruran rigakafi daga hukumar lafiya ta duniya da hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya.

Har yanzu baa san abinda wannan shawara ta Koriya ta Arewa zata haifar ba.

A halin yanzu dai Majalaisar Dinkin Duniya tana ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Koriya ta Arewan.