Koriya Ta Arewa ta ce ba ta shirin yin gwajin makami mai linzami
June 17, 2006Talla
Kasar KTA ta musanta rahotannin da aka bayar cewa tana shirin yin gwajin wani makami mai linzami dake cin dogon zango. Kamfanin dillacin labarun Japan, Kyodo ya rawaito cewa wakilan gwamnatin KTA sun tabbatarwa wani dan majalisar dokokin KTK cewar rahotannin shirin yin gwaji basu da tushe bare makama. Da farko kafofin yada labarun KTK da na Japan sun labarto cewa an tura bangarorin wani makami mai linzami dake cin dogon zango zuwa wani wurin da za´a harba shi. Gwamnatocin Amirka da Japan sun yiwa KTA kashedi da kada ta dauki wani mataki na tsokana. KTA ka iya harba irin wannan makami mai linzami dake cin dogon zango zuwa wanin yanki na Amirka.