1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta arewa ta ce ba zata koma tattaunawa na yau ba

Hauwa Abubakar AjejeAugust 29, 2005

Kasar Koriya ta arewa tace ba zata koma teburin tattaunawar shirinta na nukiliya ba.

https://p.dw.com/p/Bva8
Kim Jong il-Shugaban Koriya ta Arewa
Kim Jong il-Shugaban Koriya ta ArewaHoto: AP

Koriya ta arewan tace Ba zata koma teburin tattaunawar kafin tsakiyar satumba ba tana mai dora laifin hakan akan atisayen soji tsakanin Amurka da Koriya ta kudu,wanda gwamnatin Pyonyang tace wani sabon yunkuri ne na mamayarta.

Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu Paek Nam-Sun ya baiyana cewa,Komawar kasarsa taron ya dogara ne akan kasar Amurka,inda yace idan abubuwa sun tafi yadda ake bukata zasu koma teburin koda a karshen watan satumba ne,yace kasar Amurkan ya kamata ta soke dukkan kaidoji da ta sanya wadanda kuma suka ingiza Koriya ta kudun kera makaman nukiliya.

Kodayake manazarta sunce mai yuwa ne dalilin wannan jinkiri ba zai rasa nasaba da cewa Koriya ta kudun tana bukatar ganin sakamakon taron tsakanin China abokiyarta da kuma Amurka ba.

Wasu kuma na ganin cewa Koriya ta kudun tayi haka ne da nufin raba kawunan mahalarta taron da suka hada da kasashen Koriya ta arewa,Amurka ,Russia,Japan da Sin.

Wani dalili kuma da Koriyan ta bayar shine jakadan musamman da Amurka ta tura ne domin ya sa ido akan kare hakkin bil adama a Koriyan ya sake kawo cikas ga komawarta taron.

Ministan harkokin wajen Thailand wanda yanzu haka yake Koriya ta arewa yace yana ganin koriya ta arewa tana son nuna cewa tana iyakar nata kokari na ganin an kawo karshen wannan takaddama kamar yadda ita ma Amurka take nunawa.

Ministan ya kuma kara da cewa yayi imanin Koriya ta arewa tana son ganin an kawo karshen wannan rikici,haka zalika ta sadaukar da kanta ga ganin an sasanta cikin adalci.

Bangarorin biyu dai sun kasa cimma matsayi akan babban batu day a kawo wannan tattaunawa wato na baiwa Koriya ta arewa damar samarda shirin nukiliya.

Mahukuntan Amurkan suna dari dari da su amince Koriya ta arewa ta gudanar da aiyukan nukiliya suna masu tsaoron cewa zata yi anfani da shi ne saboda dalilan soji ko kuma ta kera makaman nukilya.

Wasu masu nazarin kuma suna ganin cewa mai yiwuwa ne Koriya ta arewan tana ganin cewa jinkirta wannan tattaunawa zai janyo rikici tsakanin kasashe 6 dake tattaunawar,wanda hakan zai kara bata damar cin karenta ba babbaka,yayinda zai kawadda kasashen shida daga kan alkiblarsu na janyo hankalinta ta dakatar da shirin nata na nukilya,ko kuma su kasa cimma matsayi guda a tattaunaar tasu.