Koriya ta Arewa ta gayyaci 'yan jarida
April 9, 2012Koriya ta arewa ta baiwa 'yan jarida wata dama wacce ba safai ta kan bada ba, domin su ziyarci cibiyar Tongchang-ri, inda take gudanar da ayyukanta da suka shafi tauraron dan adam.
Gwamnati a Pyongyang ce ta shirya wannan ziyara domin nunawa 'yan jaridan wannan makamin mai linsami wanda ake takaddama akai mai suna Unha 3 bisa zargin cewa zai iya yin ta'adi, to sai dai gwamnatin ta ce makamin zai taimaka wajen harba wani tauraron dan adam ne wanda zai taimaka wajen gudanar da bincike na kimiyya. Manema labaran dai sun ce a yanzu haka an riga an shirya makamin mai dogon zango domin harba shi kamar yadda aka tsara.
Kasashen Amurka, Koriya ta Kudu da Japan suna fargabar cewa harba wannan makami wanda ake sa ran yi a tsakiyar wannan wata na Afrilu ka iya zama wani shiri na kai harin nukiliya.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Usman Shehu Usman