Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami
March 27, 2023Talla
Kasar Koriya ta Kudu ta ce ta bi diddigin makaman da makwafciyarta Arewa ta harba. Sai dai yayin da take tabbatar da hakan, kasar Japan ta ce makaman sun sauka ne a wajen yankin tattalin arzikinta.
Kasashen biyu dai sun yi Allah wadai da matakin makwafciyarsu, kana suka ce za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana yayin da suke sa ido kan ayyukan Koriya ta Arewa.
Koriya ta Kudu ta kuma yi ikrarin ci-gaba da karfafa alaka da Amirka. A cikin wannan shekarar, kasar Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami kimanin 20 a wani mataki na tursasawa Amirka amincewa da matsayinta kan makaman nukiliya tare da neman kulla yarjejeniya domin janye takunkuman da aka kakaba mata.