Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami
May 21, 2017Koriya ta Arewa a ranar Lahadin nan ta sake harba wani makami mai linzami mai cin matsakaicin zango, kamar yadda jami'ai na Amirka da Koriya ta Kudu suka bayyana. Wannan na zama na baya-bayan nan da kasar ta harba a kokarinta na hada makamin nukiliya da makamai masu linzami.
An dai harba wannan makami ne daga kusa da yankin Pukchang na Koriya ta Arewa inda ya tashi zuwa samaniya da nisan kilomita 500 ko mil 320 a cewar jami'an hadin gwiwa na Koriya ta Kudu. Shi ma kwamandan Amirka a yankin Pacific ya ce sun gano makamin mai linzami kafin ya fada teku.
Wani jami'in fadar White House da su ke tare da Shugaba Donald Trump a ziyararsa a Saudiyya ya bayyana cewa wannan makami da Koriya ta Arewa ta harba a yau bai yi nisan da ya kai na kwanan nan ba da take harbawa.