1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahukuntan Japan sun soki Koriya ta Arewa

Zulaiha Abubakar
October 2, 2019

Rundunar sojojin Koriya ta Arewa ta sanar da harba makami mai limzami cikin tekun da ya hade yankin Koriya gabanin komawa teburin tattaunawa tsakaninta daAmirka da za a gudanar a karshen wannan mako.

https://p.dw.com/p/3QcCO
Nordkorea feuert erneut "Projektile"
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Young-joon

Jim kadan bayan harba makamin ministan tsaron Kasar Japan Taro Kono ya bayyana cewar makamin da Koriya ta Arewan ta harba ya sauka a yankin hada-hadar tattalin arzikin Japan. bayan  firaiminista Shinzo Abe ya bayyana wannan mataki da Koriya ta Arewa da dauka a matsayin karya dokokin Majalisar Dinkin Duniya, tare da shan alwashin ci gaba da goyon bayan Amirka da sauran kasashe don kare al'umma da kuma zama cikin shiri.