Koriya ta arewa ta ja kunnen koriya ta kudu a game da takunkumin MDD
October 25, 2006Talla
Koriya ta arewa ta gargadi makwabciyar ta Koriya ta kudu ta kiyayi bi sahun takunkumin karya tattalin arziki da Amurka ke jagoranta a kann Pyongyang, tana mai kashedin maida martani a kann dukkan wani mataki da Koriya ta kudun za ta dauka. An ruwaito wani mai magana da yawun kwamitin hadewar kasashen biyu na cewa shigar koriya ta kudu cikin kawance takunkumi zaá dauke shi a matsayin tunzura ce wadda zata iya kaiwa ga mummunan rikici ta fuskar yaki a tsakanin su da ma yankin baki daya. Koriya ta arewan ta taba yin makamancin wannan kashedin a cikin watan Satumba gabanin ta yi gwajin makamin nukiliyar a wannan watan wanda ya haddasa kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya kakabata mata takunkumin makamai dana matsin tattalin arziki.