1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta mayar wa Amirka martani

Abdourahamane Hassane
April 15, 2017

Mutumin da ake jin cewar shi ne mai mukami na biyu mafi girma a gwamnatin Koriya ta Arewa bayan shugaban kasar Choe Ryong Hae ya yi gargadin cewar za su mayar da martani ga Amirka idan ta kuskura ta kai musu hari.

https://p.dw.com/p/2bHS3
Nordkorea Militärparade in Pjöngjang
Hoto: picture alliance/AP Photo/W. Maye-E

Choe Ryong Hae din ya bayyana haka ne a yayin wani paretin soji da dakarun Koriyar ta Arewan suka yi domin tunawa da cikon shekaru 105 da haihuwar jagoran Koriya Kim II Sung kakan shugaban kasar mai ci yanzu Kim Jong Un. Wannan furuci dai ya biyo bayan da Amirka ta aike da wasu manyan jiragen ruwa masu harba makamai masu linzami a sansanin sojinta da ke a Koriya ta Kudu saboda shirin ko ta kwana.