Koriya ta arewa ta sake barazanar gwajin makamai masu linzami
July 6, 2006Koriya ta arewa ta sake barazanar kara wasu gwaje gwajen makamai masu linzami muddin dai kasashen duniya sunci gaba da matsa mata lamba kann gwajin makamai masu linzami guda 7 da tayi jiya.
Wata sanarwa da ministan harkokin wajen Koriya ta arewa ya fitar a yau tace kasar tana da yancin kera da kuma gwajin makamai masu linzami,ta kuma lashi takobin daukar mataki akan duk wanda yayi kokarin dakatar da ita daga gwaje gwajen nata.
Koriya ta kudu dai a nata bangare,tace zata ci gaba da hulda da koriya ta arewan.
Minista mai kula da hadewar kasashen Lee Jong Seok ya fadawa majalisar dokin kasar cewa,zaa gudanar da taro tsakanin kasashen biyu kamar yadda aka shirya tun farko,haka kuma Koriya ta kudu ba zata dakatar da harkokinta fa koriya ta arewan ba saboda wannan gwaje gwaje.