1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta sake gwagin makami mai dogon zango

Salissou Boukari
February 12, 2017

A wani abun da makwabciyarta ta Kudu ta danganta da tsokana, Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai lizzami mai cin dogon zango a matsayin gwaji zuwa ruwan kasar Japan.

https://p.dw.com/p/2XPdA
Südkorea TV-Berichterstattung zu Raketentest in Nordkorea
Gwajin makami mai cin dongon zango a Koriya ta ArewaHoto: Getty Images/AFP/J. Yeon-Je

Kasar Koriya ta Arewa ta sake gwagin wani makami mai dogon zongo a wannan Lahadin, gwajin da a cewar Koriya ta Kudu wata tsokana ce da ke nuna alamun gwada sabon shugaban Amirka Donald Trump. Sabon gwajin makamin an yi shi ne da misalin karfe 07:55 na safe agogon kasar daga barakin sojan sama na Banghyon da ke yammacin kasar, inda kuma aka harba shi zuwa gabas wajejen kasar Japan a cewar kakakin ofishin ministan Koriya ta Kudu cikin wata sanarwa, inda ya ce makami ya ci a kalla km 500 kafin ya fada cikin teku.  Sai dai tuni Firaministan kasar Japan da ke ziyara a Amirka ya soki wannan mataki inda ya ce:

" Wannan gwajin sabon makami da Koriya ta Arewa ta yi abu ne da ba za a yarda da shi ba."

Shi kuma daga na shi bangare Shugaban Amirka Donald Trump cikin wani takaitaccen bayani, ya tabbatar cewa, Amirka na goyon bayan Japan dari bisa dari dangane da wannan batu.  Dokoki da dama na MDD sun haramta wa Koriya ta Arewa yin gwajin iri-irin wadannan makammai.