Koriya ta Arewa ta sake harba makami mai linzami
March 10, 2016Ministan tsaron kasar ta Koriya ta Arewar ya bayyana cewa da misalin karfe takwas da minti 20 na agogon GMT na daran ranar Laraba ne suka kaddamar da harbin makaman masu linzamin guda biyu wadanda suka yi tafiyar kilomita 500 kafin su fada kusa da tashar jiragen ruwan Wonsan ta kasar da ke a gabar tekun Japan.
A makon da ya gabata ne dai Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya dauki matakan tsaurara takunkumin tattalin arziki kan Koriya ta Arewar a matsayin martani ga ci gaba da gudanar da ayyukanta na nukiliya duk da kashedin da take fuskanta daga kasashen duniya.
Tuni ma dai wasu kasashe irinsu Sin wato China suka yi tir kuma tuni ma dai Chinar ta dauki matakin jan kunnen Koriya ta Arewa biyo bayan sake harba makamai masu linzamin da gwamnatin Pyongyang ta yi.