Koriya ta Arewa ta sake kwajin makamai
March 3, 2016Kasar Koriya ta Arewa ta yi kwajin rokoki masu tafiyar gajeran zango a cikin tekun ta bangaren kasar da Japan. Kwajin ya zo jim kadan bayan tankunkumin da Majalisar Dinkin Duniya kara dankara wa kasar.
Moon Sang Gyun mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Koriya ta Kudu da ke kula da abin da ke faruwa ya yi karin haske:
"Da misalin karfe 10:00 na safe, sojojin Koriya ta Arewa sun harba rokoki masu tafiyar gajeran zango ta gaban gabashin tekun kasar (kusa da Japan). Saboda haka sojojinmu suna duba yanayin da ake ciki kuma suna shirye."
Daukacin mambobin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da saka takunkumin kan kasar ta Koriya ta Arewa, bayan kwashe makonni bakawai ana tattaunawa, saboda yadda kasar take watsi da duk kashedi da aka yi mata kan kwajin makamai.