1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin makamai

April 29, 2017

A wani mataki na bujire ma umarnin kasashen duniya kan haramcin gwajin makamai, Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin makami mai linzami sai dai ya tarwatse bai yi nasara ba.

https://p.dw.com/p/2c738
Nordkorea Raketentest bei Hwasong
Hoto: Reuters/KCNA

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami a yau Asabar inda ta yi watsi da kashedin Amirka da kuma China babbar aminiyarta wadda ta sha yin kokari tsawon shekaru domin takaita shirin kasar na bunkasa makaman kare dangi.

Sai dai jami'an Amirka dana Koriya ta kudu sun ce gwajin makamin wanda aka harba daga wani yanki a Pyongyang babban birnin kasar bai yi nasara ba domin ya tarwatse jim kadan bayan harba shi.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Twitter shugaban Amirka Donald Trump yace Koriya ta arewa ta nuna rashin girmamawa ga China da kuma shugaban kasar da wannan gwaji da ta yi yana mai cewa babban abin takaici ne.

Gwajin makamin na Koriya ta arewa na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren tsaron Amirka Rex Tillerson ya gargadi kwamitin sulhun majalisar Dinkin Duniya cewa idan ba'a dakile shirin nukiliyar Koriya ta arewa da kuma makamanta masu linzami ba, su na iya kaiwa ga aukuwar mummunan bala'i.

Wannan dai shine karo na hudu da Koriya ta Arewar ta ke gwajin makami mai linzami daga watan Maris din da ya gabata zuwa yau.