Koriya ta Arewa ta yi barazana kan makamai
May 19, 2017Mataimakin jakadan Koriya ta arewa a Majalisar Dinkin Duniya yace kasarsa za ta gaggauta cigaba da bunkasa karfin makamanta na nukiliya matukar Amirka ta cigaba da nuna mata manufofin kiyayya.
Kim In Ryong ya kuma yi watsi da zargin cewa Koriya ta arewa na da hannu a kutsen da aka yi na satar shiga yanar gizo da cewa kalamai ne na wauta.
Yace a duk lokacin da wani bakon abu ya faru Amirka kan nuna irin wannan halayya ta kiyayya ta kaddamar da farfaganda da gangan tare da danganta Pyongyang da lamarin.
Yace idan gwamnatin Trump na bukatar zaman lafiya a yankin tsibirin Koriya to ya kamata ta maye gurbin yarjejeniyar da ta kawo karshen yakin koriya ta 1950 zuwa 1953 da yarjejeniyar zaman lafiya ta kuma dakatar da manufofinta na kin jinin Koriya ta arewa.