Sabon gwajin makamai a Koriya ta Arewa
July 25, 2019Talla
Wannan gwaji na Koriya ta Arewa na zuwa ne yayin da kasar da Amirka ke fatan ci gaba da tattauna batun makaman nukila. Ministan tsaron kasar Japan Takeshi Iwaya ya bayyana takaicinsa game da faruwar wannan al'amari wanda ya kira da cin fuskar tanadin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Babban jami'in ya jaddada aniyar kasar Japan hadin gwiwa da Koriya ta Kudu a aikin sanya ido da tattara bayanai domin mika wa gwamnatin Amirka gabanin ci gaban tattauna batun makaman nukular Koriya ta Arewa. Ko cikin watan Mayun sai da Koriya ta Arewa ta kaddamar da wani gwajin makamai mai razanarwa.