1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami

May 19, 2013

Kasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami da ke cin gajeren zango.

https://p.dw.com/p/18ahj
Hoto: Reuters

Kasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami da ke cin gajeren zango a wannan Lahadi, kwana guda bayan kaddamar da gwaje-gwaje uku da kasar ta yi.

Kamfanin dillancin labaran kasar Koriya ta Kudu ya ce, mahukuntan na Koriya ta Arewa sun kaddamar da gwajin duk da jan kunne daga kasashen Yammacin Duniya, ko da shi ke wannan ba sabon abu bane, amma akwai matukar damuwa bisa halin tsaro a mashigin ruwan kasashen na Koriya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna damuwa da wannan gwajin makami na Koriya ta Arewa, sannan ya nemi mahukuntan Pyongyang su daina nuna irin wannan hali, kuma su koma kan teburin tattaunawa kan makaman nukiliya da kasashen duniya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh